in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da babban magatakardar MDD
2013-06-20 10:35:47 cri

A ranar Laraba 19 ga watan nan ne shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin, ya gana da babban magatakardar MDD Mr. Ban Ki-Moon, a ci gaba da ziyarar aiki da jagoran MDD ke yi a nan kasar Sin. Yayin wannan ganawa tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa, al'ummomi a fadin wannan duniya na dora kyakkyawan fatansu ga MDD, musamman duba da dinbin ayyukan da take aiwatarwa a sassan duniya daban-daban.

Xi, ya ce, tarin sauye-sauye masu sarkakiya, da kalubale maras iyaka da kasashen duniya ke fuskanta, ya wajabtawa kasashe mambobin MDD tashi tsaye, wajen yin aiki kafada-da-kafada, domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta. Bugu da kari, shugaban kasar ta Sin ya yi kira ga majalissar da ta rungumi akidun tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, adalci da bunkasa hadin kai tsakanin kasashe domin cimma moriyar juna.

Daga nan sai Xi ya bayyana kudurorin ci gaban kasarsa, yana mai fayyace irin yadda kasar ta Sin da MDD ke bukatar juna a fannin samar da ci gaba, da magance dinbin kalubalen da ake fuskanta daga dukkanin fannoni. Bugu da kari, ya ce, a matsayinta na wakiliya a MDD, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da majalissar domin cimma burikan da aka sanya gaba, ciki hadda na muradun karni, da na sauyin yanayi, da kuma tallafawa zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

A nasa jawabi, babban magatakardar MDD ya yabawa kasar Sin, bisa kokarinta na shiga a dama da ita a ayyukan wanzar da zaman lafiya, da burin cimma muradun karni na majalissar. Har ila yau, Ban ya taya kasar murnar harba sabon kunbon nan nata mai lakabin Shenzhou-10. Daga nan sai ya sake yin kira ga Sin da ta karfafa gudummawar da take bayarwa a sha'anin da ya shafi yankinta, da kuma na kasa da kasa.

Yayin wannan ganawa dai, shugabannin biyu sun yi musayar yawu don gane da rikicin kasar Sham, da kuma batun yanayin da zirin Korea ke ciki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China