Kasashen biyu sun bayyana abubuwan da suke son cimmawa ne cikin sanarwar hadin gwiwar da aka bayar a ranar karshe ta ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar ta Indiya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sassan za su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan iyakokinsu tare da warware sauran batutuwan da ke kan teburi, kafin a kai ga warware batun kan iyakokinsu.
Kasar ta indiya dai ita ce zangon karshe na ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasashe 4 na tsakiya da kudancin Asiya, ziyarar da ta kai shugaba Xi kasashen Sri Lanka, da Maldives da kuma Tajikistan inda ya halarci taron hadin gwiwa na kungiyar Shanghai.(Ibrahim)