A gun taron, an bayyana cewa, yanzu kasar Sin tana cikin muhimmin lokaci na fuskantar kyakkyawar damar samun bunkasuwa, kuma a watanni shida na karshen shekarar bana, kasar Sin za ta kiyaye samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.
A gun taron, an bukaci hukumomin wurare daban daban na kasar Sin da su ci gaba da aiwatar da manufofin kudi masu yakini da kara nuna goyon baya da matakan bunkasa tattalin arziki, yin kokarin inganta cinikin waje, kyautata manufofi da bada hidima, kara shigar da kayayyaki, yin kokarin tinkarar rikicin ciniki, da kuma sa kaimi ga kamfanoni da su zuba jari a kasashen waje. (Zainab)