in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin kasar Cuba
2014-07-23 14:31:43 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin kasar, kuma shugaban majalisar ministocin kasar Cuba Raul Castro, a birnin Havana fadar gwamnatin kasar Cuba a jiya Talata.

Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa, hanyar gurguzu ta musamman da kasar Sin ke bi, ta dace da tarihi da kuma bunkasuwar kasar Sin, don haka kasar za ta ci gaba da bin wannan hanya. Kana Sin tana goyon bayan kasar Cuba game da ci gaba da bin hanyar gurguzu.

Kaza lika shugaba Xi ya alkawarta ci gaba da baiwa jama'ar kasar Cuba tabbaci na kiyaye mulkin kan kasarsu, tare da ba da taimako ga kasar wajen aiwatar da kwaskwarimar tsarin tattalin arziki.

Bugu da kari, kasar Sin na fatan ci gaba da mu'amala ta fuskar shawarwari, tsakanin shugabanninta da takwarorinsu na Cuba, da gudanar da hadin kai bisa manyan batutuwa na cimma moriyar juna, tare da karfafa musayar ra'ayi, kan kyautata tsarin gurguzu da na zaman takewar al'umma, da kuma tsarin kwaskwarima a fannoni daban daban.

A nasa bangare Mr. Castro ya bayyana cewa, kasarsa na matukar godiya game da goyon bayan da Sin take nunawa Cuba. Castro ya kara da cewa kasar Cuba za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen nuna goyon baya ga kasar Sin kan kiyaye mulkin kai, da tsaro, da kuma cikakken ikon yankunan kasar, baya ga fatan karfafa mu'amala da Cuba ke burin yi da Sin, ta fuskar fasahohin kyautata tsarin gurguzu tare da kasar Sin.

Mr. Castro ya kara da cewa, kasar Cuba na mai da hankali sosai kan dangantakar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, tare da burin ci gaba da raya hadin gwiwarta da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aiki hakar ma'adinai, da sashen makamashi na bola-jari, da aikin noma da dai sauransu.

Har ila yau a cewar Mr. Castro, kasar Cuba na maraba da zuba jarin da kamfanonin kasar Sin suka yi ko za su yi a kasar, ya kuma gabatar da shawarar kafa wasu tawagogin aikin musamman, don ciyar da manyan ayyukan hadin gwiwar sassan biyu gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China