A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar tattalin arziki shi ne hanyar da ta sa kaimi ga bunkasa kasashe membobin kungiyar ta BRICS, don haka ya kamata a bi ka'idojin bude kofa, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa, sannan kuma da samun moriyar juna, da yin kokari wajen raya kasuwa mai tsarin bai daya, kara yin musayar kudi, yin hadin gwiwa wajen gina ayyukan more rayuwa, yin mu'amala a fannin al'adu, tsara shirin yin hadin gwiwar tattalin arziki a dogon lokaci, sannan raya dangantakar abokantaka a fannin tattalin arziki a tsakaninsu. Har ila yau ya jaddada cewa, ya kamata a gaggauta kafa bankin raya kasashe membobin kungiyar BRICS da tsara shirin ajiye kudi don tinkarar halin dokar ta bace.
Hakazalika shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kamata ya yi kasashe membobin kungiyar BRICS su sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya, kana su yi kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu da sauran kasashen duniya a fannonin siyasa da tsaro don tabbatar da samun adalci a duk fadin duniya.
Ban da wannan kuma, shugaba na kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, kamata ya yi kasashe membobin kungiyar BRICS su kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu da sauran kasashen duniya, da kuma kara samun ikon yin magana kan harkokin tattalin arzikin duniya. (Zainab)