Ranar 15 ga wata, a birnin Brisbane na kasar Australia, an bude taron koli karo na 9 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20.
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci taron tare da ba da wani muhimmin jawabi mai taken "kara azama kan aikin kirkire-kirkire da bunkasuwa, a kokarin samun ci-gaba tare", inda ya yi kira da a zama abokan juna da ke sa kaimi kan yin gyare-gyare a harkokin tattalin arziki, da kuma aiwatar da manyan tsare-tsaren bunkasuwa daga dukkan fannoni, a kokarin kara azama kan ganin tattalin arzikin duniya ya samu ci-gaba mai dorewa, a maimakon samun farfadowa ta lokaci-lokaci. Har wa yau shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda take yi a halin yanzu, a kokarin kara ba da gudumowa wajen raya tattalin arzikin duniya.
Haka zalika, shugaban na kasar Sin ya shawarci kungiyar ta G20 da ta ba da nata kokari a fannoni 3, wato sabunta hanyar bunkasuwa, raya tattalin arzikin duniya da ke bude kofa ga kowane bangare, da kyautata yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya.
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar sun yaba wa yadda kasar Sin take kokarin kyautata tsarin tattalin arziki, da sauya hanyar raya tattalin arziki cikin himma. Sun yi imanin cewa, zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin take yi daga dukkan fannoni zai taimaka wa kasar ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki yadda ya kamata, wadda za ta kara ba da babbar gudummowa wajen raya tattalin arzikin duniya.
Sakamakon kokarin da kasashen Sin da Amurka da Australia suka yi ya sa an zartas da sanarwar Brisbane dangane da yaki da cutar Ebola, inda aka yaba wa babbar gudummowar da kasashen duniya suke bayarwa, tare da yin kira da su inganta hada kan juna wajen yaki da cutar cikin hadin gwiwa. (Tasallah)