Xi ya ce kamata ya yi a yi biyayya ga kudurorin cikakken zama na uku da na hudu, na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sa kaimi ga samun wadata a kasar, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da kuma gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, da kiyaye bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar, da kuma kara samun ci gaba.
Xi Jinping ya nuna cewa, kara kyautata halayen 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin, da daukar tsauraran matakai wajen gudanar da harkokin jam'iyyar yadda ya kamata, kana su ne tushen gudanar da ayyuka a dukkan fannoni. (Zainab)