Bayan ganawar tasu, a gaban shugabannin kasashen biyu, ministan ciniki na kasar Sin Gao Hucheng, da ministan ciniki da zuba jari na kasar Australia Andrew Rob, sun wakilci gwamnatocin kasashen biyu, wajen rattaba hannu kan sanarwar kudurin kasashen biyu game da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci.
An kaddamar da shawarwari kan yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tsakanin Sin da Australia a watan Afrilun shekarar 2005. Shawarwarin na wannan karo dai na da matukar muhimmanci, wanda Sin ta kammala tsakaninta da wata muhimmiyyar kasar mafi ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific a wannan fanni, bayan da aka kammala shawarwari a tsakanin Sin da Koriya ta Kudu.
Bisa sakamakon da aka samu a gun shawarwarin, Australia ta soke dukkan harajin da ake biya kan kayayyakin kasar Sin, kuma Sin ta soke harajin da ake biya kan yawancin kayayyaki daga kasar Australia. Kaza lika kasashen biyu sun yi alkawarin bude kofa ga juna a fannin bada hidima mai inganci dake shafar hukumomi da dama.
A fannin zuba jari ma, kasashen biyu za su samar da rangwame ga juna tun daga ranar da za a fara aiwatar da yarjejeniyar. (Zainab)