A ranar Litinin 17 ga wata a majalisar dokokin kasar Australia, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi mai taken "yin kokari tare don cimma burin Sin da Australia da samun zaman lafiya da wadata a kasashen biyu", inda ya gabatar da hanyar raya kasar Sin cikin lumana da manufofin raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen yankin Asiya da tekun Pasific.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan samun bunkasuwa cikin lumana. Bugu da kari Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa tare. Sannan kuma kasar Sin tana kokarin sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakaninta da yankin Asiya da tekun Pasific. (Zainab)