A jawabinsa shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da kasar Amurka da nufin aiwatar da manufofin mutunta juna,rashin tsokanar juna,yin hadin gwiwa tare da kulla wata sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu wadda za ta kai ga samar da moriya ga al'ummomin kasashen biyu da ma duniya baki daya.
Shugaba Xi ya ce,wannann sheakar ita ce cikon shekaru 35 da kulla dangantaka tsakanin Sin da Amurka,kuma wannan dangantaka ta kasance wani mafarin huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Shi ma da ya ke jawabi shugaba Obama na Amurka ya taya shugaba Xi da al'ummar Sinawa murna bisa nasarar gudanar da taron kolin kungiyar APEC, kana ya mika godiya ga irin tarbar da aka yi masa a yayin ziyarar aikin da ya kawo nan kasar Sin.
Obama ya ce, kasashen biyu sun shafe sama da shekaru 35 suna huldar cinikayya da musaya tsakanin al'umominsu.
A ranar Litinin ne shugaba Obama ya iso nan birnin Beijing na kasar Sin don halartar taron shugabanin kungiyar APEC karo na 22 da aka gudanar a nan Sin bisa gayyatar shugaba Xi Jinping na kasar Sin.(Ibrahim)