A yayin taron, shugaba Xi ya yi jawabinsa mai muhimmanci, inda ya jaddada cewa, kafa yankin tattalin arziki na hanyar siliki da hanyar siliki a yankin teku na karnin 21 ya dace da bukatar zamani da burin kasa da kasa na neman samun bunkasuwa, kuma ya bayar da wani babban dandalin bunkasuwa mai kunshe da sassa daban daban, wanda yake da dogon tarihi da babban tushen al'adun bil'adam, a sabili da haka, ya iya hada da tattalin arzikin Sin dake bunkasa cikin sauri da moriyar sauran kasashen dake dab da wannan hanya a gu daya. Kamata ya yi a gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, a kokarin sada zumunci da samun amincewa da goyon baya daga kasashen dab da hanyar.(Fatima)