Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron koli na kungiyar G20 karo na tara da zai gudana a watan Nuwamban bana a birnin Brisbane na kasar Australiya, kana zai kai wani rangadin aiki a kasashen Australiya, New Zealand da kuma Fiji. Taron zai gudana a ranakun 15 da 16 ga wata, kana rangadin aikin shi kuma zai gudana a ranakun 16 da 23 ga wata, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang a ranar Jumma'a.
Shugaba Xi Jinping zai gana da shugabannin kasashen yankin Pasifik dake da huldar diplomasiyya tare da kasar Sin, in ji mista Qin
Mista Xi zai yi wannan rangadi bisa goron gayyatar babban gwamna da faraministan kasar Australiya Peter Cosgrove da Tony Abbott, da kuma babban gwamna da faraministan New Zealand Jerry Mateparae da John Key, da kuma shugaba da faraminstan kasar Fiji Epeli Nailatikau da Voreqe Bainimarama. (Maman Ada)