in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta alkawarta sanya dalar Amurka biliyan 40 a Asusun bunkasa hanyar siliki
2014-11-08 20:10:39 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, kasarsa za ta sanya zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 40 ga asusun bunkasa hanyar siliki, domin kau da matsalolin dake dakile yunkurin da ake yi na hade kasashen yankin hanyar silikin ta fuskar kasuwanci da cinikayya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin da wata tattaunawar da ya yi da shugabanin kasashen Bangledesh, da Cambodia, da Laos, da Mongolia a nan Birnin Beijing.

Ya kuma kara da cewa, asusun bunkasa hanyar siliki zai samar da babbar dama ga masu sha'awar zuwa jari daga kasashen Asiya da ma sauran sassan duniya.

Sauran shuwagabannin da suka halarci tattaunawar da shugaba Xi sun hada da shuwagabannin kasashen Myanmar da Pakistan da Tajikistan, da kuma wakilai daga hukumar MDD mai lura da harkokin tattalin arziki da zamantakewar Asiya da yankunan Fasifik, da kuma wakilan kungiyar hadin kai ta Shanghai. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China