in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsaya daya a taron kungiyar APEC
2014-11-11 21:34:00 cri
A yammacin ranar 11 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron manema labaru dangane da taron shugabannin kungiyar hadin kan Asiya da tekun Pasifik a fannin tattalin arziki na shekarar 2014, inda ya yi jawabi.

A cewar shugaban, an kawo karshen taron shugabannin kungiyar APEC karon 22 tare da cimma nasara, ganin yadda shugabanni mahalarta taron suka yi musayar ra'ayoyinsu, dangane da wasu manyan batutuwan da suka hada da babban jigon taron, na kafa huldar abota a Asiya da yankin tekun Pasifik domin nan gaba, da dunkule kasashen shiyyar waje guda a fannin tattalin arziki, da raya tattalin arziki, da gudanar da gyare-gyare don samun ci gaba, da kara gina kayayyakin more rayuwa don hada kasashen shiyyar, da dai makamantansu.

A yayin taron, shugabannin sun kuma tattauna batun da ya shafi hadin gwiwar tattalin arziki a shiyyarsu, tare da cimma kyakkyawar matsaya. Shugaba Xi ya kara da cewa, a wajen taron an zartas da yarjejeniyar Beijing, wadda ta shafi kara hada kan kasashen dake Asiya da yankin tekun Pasifik, gami da sanarwar cikar shekaru 25 da kafuwar kungiyar, wadanda suka kasance manyan sakamako guda 2 da aka samu a taron. Wadannan takardun yarjejeniyoyi za su tabbatar da burin shiyyar, da kuma matakan da za a dauka a nan gaba, in ji shugaban. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China