A yayin da ake tattaunawa kan yadda za a iya karfafa karfin tattalin arzikin kasa da kasa wajen fuskantar kalubaloli daban daban, shugaba Xi ya bayyana cewa, da farko, ya kamata a ci gaba da aiwatar da kwaskwarima kan tsarin sha'anin kudin duniya, da kuma gaggauta yunkurin gyare-gyaren tsarin hannun jari na asusun ba da lamuni na IMF. Sa'an nan kuma, ya kamata a karfafa hadin gwiwa kan aikin kudin haraji na kasa da kasa, domin yaki da kaucewa biyan haraji da kuma taimaka wa kasashe masu tasowa da kasashe masu karancin kudaden shiga wajen inganta karfinsu kan ayyukan dake shafar wannan fanni. Bugu da kari, ya kamata a zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa. Haka kuma, a kara mai da hankali kan harkokin neman bunkasuwa, a gabatar da tunanin neman dauwamammen ci gaba yadda ya kamata, kana a ba da taimako ga kasashe masu tasowa.
Kaza lika, a yayin taron, an sanar da shirya taron shugabannin kungiyar G20 na shekarar 2016 a kasar Sin. (Maryam)