A lokacin wata wayar tarho da shugaba Barrack Obama a ranar talatan nan, shugabannin biyu duk sun amince akan bukatar a fuskanci munanan ayyukan da 'yan tawayen kungiyar ISIL ke yi, a kuma maida hankali sosai wajen taimakawa al'ummar kasar Iraqi da suka hada da ba da kayayyakin jin kai, in ji sanarwar da ofishin firaministan ta fitar.
Haka kuma Mr. Harper ya nuna shirin kasarsa na bada taimako idan hakan ya taso.
Shugabannin biyu suna da aniyar ganin an samar da sabuwar gwamnati a Iraqi da za ta iya hada kan al'umma wuri daya ta kuma dakile duk wani rikici da zai taso. Shugabannin biyu har ila yau sun amince su rika tuntubar juna a koda yaushe.(Fatimah)