in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka na tunanin ceton 'yan Iraqi farar hula, wadanda aka yiwa kofar raggo
2014-08-14 15:09:14 cri
A halin da ake ciki shugaban kasar Amurka, Barack Obama na duba yiwuwar kafa wani sansani na taimakon agaji a Iraq da kuma ceton jama'a ta jirgin sama domin a kwashe farar hula na Iraqi, wadanda kungiyar 'yan tsageran Islama suka yiwa kofar raggo a bisa wani tsauni.

Mataimakin mai bada shawara al'amurran tsaro akan muhimman bayanai na Amurka Benjamin Rhodes, ya ce ana bukatar magance matsalar da 'yan Iraqi farar hula suka shiga duk da kasancewar cewar jiragen saman yaki na Amurka suna ci gaba da jefa wa 'yan Yazidi, wadanda ke kan tsaunin Sinjar agajin abinci da ruwan sha da sauran kayayyakin da ake bukata, domin taimaka masu.

Rhodes ya ce, Obama zai yanke shawara a bisa la'akari da abin da ke faruwa a tsaunin Sinjar, a 'yan kwanaki kadan masu zuwa domin daukar matakan da suka fi dacewa bayan ya saurari shawarwari daga sojojin Amurka 130, masu bada shawara wadanda ba'a dade da tura su cikin kasar ta Iraqi ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China