A cewar wani mai magana da yawun jami'an kasar tsagin kurdawa, mayakan kungiyar ta ISIS mai alaka da Al-Qaida, sun hallaka Yazidawan ne a gidan wani jagoransu dake kauyen Kocho, mai nisan kilomita 100 yamma da birnin Mosul.
Jami'in tsaron ya kuma shaidawa manema labaru cewa mayakan na ISIS sun hallaka mutanen ne saboda sun ki su rungumi addinin musulunci.
Kaza lika wannan jami'i ya ce akwai wasu mutanen su sama da 200, da suka hada da mata da kananan yara, da 'yan ISISn din suka yi garkuwa da su daga kauyen Tal Afar dake karkashin ikon su.
Kafin hakan dai rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan wannan kungiya ta masu kaifin kishin Islama, sun samu nasarar kwace garin Sinjar mai rinjayen Yazidawa, matakin da ya tilasawa al'ummun garin da ma na kauyukan dake kewayen sa arcewa zuwa tsaunukan dake kewayen yankin, da wasu garuruwa masu kusanci da yankin Kurdistan. (Saminu Alhassan)