in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamanti 25 sun rasu a arangamar da ta auku tsakanin su da 'yan aware a kusa da babban birnin Iraqi
2014-06-29 17:19:00 cri
Rahotanni daga rundunar 'yan sandan kasar Iraqi na cewa a kalla sojojin gwamnatin kasar 25 ne suka rasa rayukansu, yayin wani dauki ba dadi da ya auku tsakaninsu da mayakan kungiyar 'yan sunni ta ISIS a arewacin lardin Babil dake kudancin birnin Baghdad.

Kaza lika majiyar 'yan sandan ta ce dakarun sojin gwamnatin na kan hanyar su ta zuwa birnin Tikrit dake lardin Salahudin, domin fatattakar dakarun sunni masu adawa da gwamantin kasar, wadanda suka mamaye wannan birni.

An dai ce tuni dakarun gwamnatin dake cikin jerin motocin soja, da tankuna, da jirage masu saukar ungulu suka fara fafatawa da dakarun na ISIS.

Tun dai a ranekun 10 da 11 ga watan nan ne mayakan kungiyoyin 'yan aware a Iraqin, suka mamaye manyan biranen Mosul da Tikrit da ke arewacin kasar, inda suka rika musayar wuta da sojojin gwamnati a wurare da dama, lamarin da ya haifar da kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China