Kwamitin tsaron ya samu kwarin gwiwwa ne sakamakon shawarar da shugaban kasar na Iraqi Fuad Masum ya yanke na nada sabon firaminista, in ji wata sanarwa ga manema labarai.
Wannan nadin sabon Firaministan wani muhimmin cigaba ne wajen kafa gwamnatin da zai rungumi kowa a al'ummar kasar kuma zai taimaka wajen samar da mafita mai dorewa a kalubalen da kasar take fuskanta a yanzu, in ji kwamitin mai wakilai 15.
Har ila yau kwamitin ya kuma bukaci wanda aka nada a matsayin Firaministan Haider al-Abadi da ya yi aiki tukuru domin kafa irin wannan gwamnati nan take ba tare da bata lokaci ba, kuma a cikin lokacin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Al-Abadi dan majalissar dokoki a tsohuwar gwamnatin Nuri al-Maliki na jam'iyyr Dawa yana da kwanaki 30 na nada sabuwar gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Sai dai Al Maliki tun da farko a kokarin cigaba da rike mukamin sa bai amince da nada al Abadi ya gaje shi ba wanda Shugaba Fuad ya yi wani yunkuri da masu fashin baki ke ganin ka iya sake jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Yan majalissar gudanarwar kasar sun nuna goyon bayan su ga sabuwar gwamnatin demokradiyya a Iraqin, sannan al'umar kasar su yi kokarin yakar ta'addanci musamman kungiyar jihohin isilama ta ISIL, wanda renon kungiyar al'Qaida ce. (Fatimah)