Ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta ba da sanarwa cewa, Amurka ta kai hari a birnin Erbil dake arewacin kasar zuwa kashi biyu, harin farko an kai shi da misalin karfe 10 na safe ta yin amfani da jiragen sama na yaki wanda ya taimaka wajen murkushe wata tashar harbar rokoki ta mayakan kishin islama, yayin hari na biyu aka kai shi da misalin karfe 11 da mintoci 20 na safe ta yin amfani da jiragen sama na yaki sumfurin F/A-18 guda hudu, wanda ya taimaka ga murkushe ayarin motocin yaki da wata tashar harbar rokoki na mayakan.
Kafin wannan kuma, sojin Amurka sun kai harin sama a karon farko a ranar 8 ga wata da misali karfe 6 da mintoci 45 na safe, jiragen sama na yaki suamfurin F/A-18 guda biyu sun harba boma-bomai biyu kan sansanin harbar rokoki da masu tsatsauran ra'ayi suke amfani da shi wajen kai hare-hare kan sojin dake tsaron Kurdawan birnin Erbil, wurin dake kunshe 'yan kasar Amurkawa da dama, dalilin da ya sa sojojin Amurka suka kai hare-haren wurin domin kare su in ji kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka. (Amina)