Ya ce, ya zuwa ranar 15 ga wata, kwanaki 42 sun riga sun wuce ba tare da gano karin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ba, lamarin da ya nuna cewa, an kawo karshen cutar Ebola a kasar. Kana, kasar za ta ci gaba da kafa wasu tawagogin agajin gaggawa a cibiyar dake kula da yaduwar cutar Ebola domin fuskanta da sake barkewar cutar a kasar, idan har akwai bukata.
A watan Agusta na shekarar bana, kasar Congo-Kinshasa ta sanar da gano mai dauke da cutar Ebola a lardin Equateur na kasar, a yayin da cutar Ebola take yaduwa da sauri cikin wasu yankunan dake yammacin nahiyar Afirka. (Maryam)