Mutane 48 wadanda daga cikinsu 22 sojojin MDD ne aka killace a wani asibitin Pasteur dake birnin Bamako, inda aka gano mutum na biyu da ya kamu da cutar Ebola a kasar Mali, in ji shugaban wannan asibiti, dokta Ben Baba, a yayin wani taron manema labarai a birnin Bamako. Tawagar wanzar da lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) ta tabbatar a cikin wata sanarwa cewa, wasu sojojinta kusan ishirin, da aka karbe su domin samun jinya a asibitin Pasteur a cikin watan Oktoba bayan sun samu raunuka a yayin da suke aikin sintiri a arewacin kasar Mali, a yanzu haka suna cikin wannan asibiti. (Maman Ada)