A sakamakon cutar Ebola da ta yi tsanani a yankin yammacin Afirka, kasar Senegal ta sanar da rufe iyakar kasa a tsakaninta da kasar Guinea a ranar 21 ga watan Agusta, kana ta hana shigar da jiragen sama da na ruwa daga kasashen Guinea, Saliyo da Liberia a cikin kasar.
A ranar 6 ga wannan wata, kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron kolinta a birnin Accra dake kasar Ghana, inda ta yi kira ga kasashe membobin kungiyar da su kara sa ido kan iyakar kasa a fannin lafiyar jikin mutum, da soke matakan rufe iyakar kasa don tabbatar da yin zirga-zirgar mutane da kayayyaki a tsakanin kasashe membobin kungiyar. Yadda kasar Senegal ta amince da shigar da jiragen sama da na ruwa daga kasashe masu fama da cutar Ebola a cikin kasar, wannan ya nuna amsa kiran da kungiyar ECOWAS ta yi. (Zainab)