Bisa labarin da jaridar Cameroon Tribune ta bayar, an ce, bisa kiran da kungiyar AU da bankin raya Afirka wato AFDB suka yi, shugabannin bangaren ciniki na kasashen Afirka sun gudanar da taro a birnin Addis Ababa dake kasar Habasha a kwanakin baya, inda suka tsaida kudurin kafa asusun yaki da cutar Ebola da zai bukaci dala miliyan 28.5 don tura likitoci a kalla dubu daya zuwa kasashen Guinea, Liberia da Saliyo inda za su bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar Ebola. Kuma bankin AFDB ne zai tafiyar da harkokin asusun.
Ya zuwa yanzu, bankin AFDB ya bada kudi dala miliyan 223 don taimakawa wajen yaki da cutar Ebola. (Zainab)