in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya ja hankalin kungiyar G20 game da dakile yaduwar Ebola
2014-11-15 15:47:15 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya ja hankalin mahalarta taron kungiyar kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki ta G20, game da muhimmancin zage damtse wajen yaki da cutar Ebola.

Mr. Ban wanda ya yi jan hankalin yayin wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Brisbane, ya kara da cewa, a wannan lokaci da yaduwar wannan cuta ke raguwa a wasu yankuna, a hannu guda wasu bangarorin na fama da karuwar masu kamuwa da ita, don haka ne a cewarsa, ya wajaba ga shuwagabannin G20n su kara kwazo wajen ba da gudummawar dakile cutar baki daya.

Cikin matakan da Mr. Ban ya ba da shawarar dauka domin cimma wannan buri dai, akwai batun shawo kan matsalar da kiwon lafiya ke fuskanta, da harkar ilmantarwa, da ta magance tsadar kayan abinci sakamakon kalubalen da ayyukan noma suka fuskanta.

Ya ce, MDD na da matakai 5 na yaki da yaduwar Ebola, wadanda suka hada da batun dakile barkewar ta, da yi wa wadanda suka kamu da ita magani, da samar da muhimman ayyuka domin hakan, da tabbatar da dorewar yanayin da ake ciki, tare da kare ci gaba da yaduwar ta.

Ya zuwa ranar Juma'a, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, mutane 5,177 ne Ebola ta hallaka cikin kasashe 8 da ta bulla, daga jimillar mutane 14, 413 da aka hakikance sun kamu da cutar tun daga watan Disambar bara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China