Kasashen da suka fi fama da cutar Ebola suna fuskantar barazanar karancin abinci in ji MDD
Mai isar da rahoto ta musammun ta MDD kan 'yancin samun abinci, Hilal Elver ta yi kashedin cewa annobar cutar Ebola a yammacin nahiyar Afrika da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu hudu, yanzu tana barazanar wannan shiyya da wata matsalar karancin abinci dalilin faduwar albarkatun noma. A yayin da kasashen dake fama da cutar Ebola suke kokarin magance cutar, yanzu kuma suna fama da wani sabon kalubale a yayin da kuma kwararru suka yi gargadin cewa fiye da mutane miliyan daya dake wannan shiyya suna bukatar taimakon abinci domin cike gibin karancin abinci in ji madam Elver.
Manoman dake yammacin Afrika sun yi fama sosai da wannan matsala, tsoro da fargaba sun tilastawa yawanci daga cikinsu barin gonakinsu, lamarin da ya janyo illa ga samar da albarkatun noma tare da kuma janyo hauhawar farashin abinci. Girbin albarkatun noman da ake samu, musammun shimkafa da masara zasu yi kasa sosai dalilin rashin manoma, tare da yiyuwar janyo bala'in karancin abinci in ji madam Hilal Elver. (Maman Ada)