A halin da ake ciki kungiyar tarayyar Afrika AU ta aike da tawagar kwararru a fannin kiwon lafiya, wadanda suka hada da likitoci da masu kula da marasa lafiya zuwa Liberia domin yaki da cutar Ebola mai saurin kisan jama'a.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Liberia ta ce, tawagar ta kungiyar tarayyar Afrika ta kunshi kwararrun kiwon lafiya daga gabashi da yammacin Afrika, kuma tawagar za ta yi aiki a karkashin hadin gwiwar kasashen Afrika na bayar da tallafi a sakamakon bullar cutar Ebola a Afrika ta yamma ASEOWA.
Tawagar za ta samar da taimako na jin kai a fannin kula da marasa lafiya, da kuma bayar da horo, tare da bayar da goyon baya wajen nazarin cutar, da kuma kwantar da hankulan jama'a, musamman a kasashen da cutar ta yi kamari.
Shugaban tawagar ta kungiyar tarayyar Afrika, Manjo Janar Julius Oketta ya ce, za'a rarraba kwararrun a wuraren da cutar ta Ebola ta yi kamari da nufin taimakawa wajen dakile cutar ta Ebola. (Suwaiba)