in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karin wasu likitocin kasar Sin sun isa Saliyo
2014-11-11 17:04:55 cri
Da misalin karfe 7 na daren ranar Lahadin da ta gabata ne wasu karin likitocin kasar Sin 21, masu kula da lafiya da masu binciken kwayoyin cutar Ebola suka isa birnin Freetown, fadar mulkin kasar Saliyo.

Wadannan likitoci dai na cikin jerin tawagogin likitocin kasar Sin na 2, wadanda kasar ta tura Saliyo domin tallafawa kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar Ebola.

A cewar shugaban tawagar likitocin kasar Sin masu kula da binciken kwayoyin cuta ta dakunan gwaje-gwaje na tafi-da-gidanka Liu Chao, babban nauyin dake wuyan tawagar ta 2 shi ne, amfani da dakunan gwaje-gwaje na musamman don binciken kwayoyin cutar ta Ebola.

Sauran likitocin kasar Sin dake wannan tawaga ta 2 za su isa kasar Saliyon ne nan da ranar 15 ga wata. Idan an kwatanta da tawagar farko dai, ana iya cewa an inganta tsarin tawagar ta 2 kwarai a dukkan fannoni, da suka hada da likitoci masu kwarewa, da yadda aka raba su cikin rukunoni daban daban, da ayyukan da za su gudanar, da dai makamantansu.

Kana kafin sun tashi zuwa kasar Saliyo sun riga sun yi gwajin ayyukasu na binciken kwayoyin cutar ta Ebola, da aikin jinyar masu dauke da cutar, da kandagarkin kamuwa da cutar, da dai sauransu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China