in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shuwagabannin G20 sun alkawarta taimakawa yaki da Ebola
2014-11-15 20:35:20 cri
Shugabannin kungiyar G20 sun sha alwashin hada karfi da karfe wajen yaki da cutar Ebola, cutar da yanzu haka ke shafar sassan tattalin arziki, baya ga kasancewar ta babbar barazana ga harkokin kiwon lafiyar duniya.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mahalarta taron G20 suka fitar a Asabar din nan. Sanarwar ta kuma bayyana aniyar kasashe mambobin kungiyar game da hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki, domin murkushe wannan cuta.

Cikin matakan da G20 za ta dauka a wannan fage hadda musayar dabaru, da bunkasa bada horo tare da tabbatar da kare lafiyar ma'aikatan lafiya, dake bada agaji ga yankuna masu fama da yaduwar cutar.

A daya bangaren kuma sanarwar ta bukaci bada kulawa ga harkar bincike, da samar da sahihan magunguna, da alluran rigakafi, da kayan aikin magance Ebola.

Bugu da kari shuagabannin kungiyar ta G20 sun yi kira ga bankin duniya da asusun bada lamuni na IMF, da su ci gaba da tallafawa kasashen dake fama da yaduwar wannan cuta. Kaza lika kungiyar ta jinjinawa IMF, bisa assasa shirin samar da zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 300, domin yaki da Ebola, tare da sassauta halin da kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo ke ciki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China