Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta sanar da dage dokar ta bacin da aka sanya a baya sakamakon barkewar cutar Ebola a kasar ba tare da bata lokaci ba.
Shugabar ta bayar da wannan sanarwa ce a jiya Alhamis, inda ta ce, an dauki wannan mataki ne saboda irin ci gaban da aka samu ya zuwa wannan lokaci bayan tuntubar bangarorin da suka kamata, da kuma abokan hulda na gida da waje da ke aikin magance wannan cuta a kasar.
Ta ce, wannan ba wai yana nufin an kawo karshen yakin da ake da cutar ba ne, sai dai kasar ta sake daura damara har sai ta ga bayan cutar kwata-kwata.
Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar kasar ta bayar a ranar Litinin ta nuna cewa, an aika sanfurin masu dauke da cutar 126 zuwa dakunan gwaji biyar din da ake da su a kasar, inda aka gano 54 suna dauke da cutar yayin da ba a gano matsayin na mutane guda 9 ba.
Alkaluman hukumar lafiya ta duniya na nuna cewa, sama da mutane 5,100 ne suka mutu sakamakon cutar ta Ebola a yammacin Afirka, yayin da cutar ta halaka mutane 2,836 a kasar Liberia. (Ibrahim)