in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi atisayen tinkarar cutar Ebola a wurare daban daban na kasar Sin
2014-11-13 15:46:33 cri
A kwanakin baya ne, aka yi atisayen tinkarar cutar Ebola a biranen Beijing, Shanghai, Hongkong da sauran birane na kasar Sin. Kakakin hukumar kiwon lafiya da kyayyade iyali ta kasar Sin Song Shuli ta bayyana wa manema labarai cewa, a shekarun baya, kasar Sin ta bullo da tsarin kula da cututtuka masu yaduwa, baya ga kara inganta tsarin rigakafi da yaki da cututtuka da bada jinya. A halin yanzu, kasar Sin tana da karfin yin rigakafi da yaki da cutar Ebola.

A gun bikin rufe kwarya-kwaryar taron kungiyar APEC karo na 22 da aka yi a kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da ake kokarin fama da cutar Ebola dake yaduwa, shugabannin mambobin kungiyar APEC sun tsaida kudurin hadin gwiwarsu don taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar cutar da kuma shawo kanta, baya ga nuna goyon baya ga MDD da ta bada gudummawa ga kasashen Afirka da taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar Ebola, da kuma bada taimako ga jama'ar dake yankuna masu fama da cutar Ebola don tinkarar cutar har zuwa lokacin da za a kawar da ita. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China