Qian Keming ya bayyana haka ne a yayin zaman tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka karo na biyar da ake yi a birnin Wanning na kasar Sin, a yau Jumma'a, yayin taron karawa juna sani kan hadin gwiwar aikin noma tsakanin Sin da Afirka, Mr. Qian ya yi bayani cewa, aikin noma shi ne tushen bunkasuwar zaman takewar al'umma, akwai isassun filayen noma da kuma hasken rana a nahiyar Afirka, lamarin da ya dace da raya aikin noma a Afirka sosai, kana kasar Sin na da fasahohin noma na zamani, shi ya sa hadin gwiwar Sin da Afirka kan harkokin noma ta dace da moriyar juna sosai, ta yadda za su iya kyautata harkokin noman bangarorin biyu bisa taimakon juna.
Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga kulla yarjejeniyoyi da dama tare da kasashen Afirka guda 17 da wasu kungiyoyin da abin ya shafa, gaba daya ta ba da taimako wajen gina cibiyoyin fasahohin aikin noma guda 22 na gwaji, kana ta aike da manyan masanan aikin noma da dama zuwa Afirka, sannan ta horas da 'yan Afirka sama da dubu 5 kan harkokin tattalin arzikin noma da fasahohin noma a kasar Sin. (Maryam)