Mr. Ssekandi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wakilan tawagar aikin gon ta lardin Sichuan na kasar Sin. Inda ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasarsa na son ciyar da zamanintar da kayayyakin ayyukan gona gaba, da kuma samar da karin hatsi, kasar Uganda na maraba da kasar Sin da ta kara zuba jari a kasar musammun ma a wannan fanni, tare da fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ta fuskar aikin gona. (Maryam)