in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe masu tasowa 38 sun tura jami'ansu zuwa nan kasar Sin domin tattaunawa kan batun hadin gwiwa wajen sha'anin noma
2013-09-13 16:00:04 cri

Manyan jami'ai kimanin 100 daga kasashe masu tasowa 38 sun isa birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin a ran 12 ga wata domin halartar taron tattaunawa kan hadin gwiwa a sha'anin gona, bisa burin sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin wajen sha'anin noma daga dukkan fannoni ta hanyar tuntubar juna a fannin bayanai, nazarin hanyar da za su bi ta hadin kai, yin musayar ra'ayi kan kimiyya da fasaha.

Yayin taron, jami'ai masu kula da sha'anin gona na wadannan kasashe sun bayyana halin da suke ciki a wannan fanni, tare kuma da nuna kyakkyawar fata na son yin hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin.

Ministan sha'anin gona na kasar Mozambique Jose Pacheco ya nuna fatansa na hadin gwiwa da kasar Sin a fannin kayan amfanin gona ciki hadda wake, ayaba da sauransu, tare kuma da nazarin kimiyyar shuka shimkafa.

Jami'in ma'aikatar kasuwanci da masana'antu ta kasar Lybia ya furta cewa, yana fatan kara samun yawan amfanin gona da kudin shiga ga manona ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha masu inganci na kasar Sin.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa yanzu, yawan masanan sha'anin noma da Sin ta turawa kasashe masu tasowa na nahiyar Asiya, Afrika, Latin Amurka da sauran wurare ya kai kimanin dubu daya, tare kuma da kafa cibiyoyin aikin gwaji na sha'anin gona kimanin 20, wadanda suka horar da mutane sama da 16000. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China