in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen yammacin Afrika da su kara zuba jari cikin ayyukan noma da ruwa
2013-12-11 12:14:39 cri

Bankin cigaban yammacin Afrika na BOAD ya yi kira ga kasashen mambobin hukumar kudin da su kara zuba jari tare da taimakon kungiyoyin ba da tallafin kudi da fasaha a cikin harkokin noma da ruwa da kuma kawo sauye-sauyen da suka wajaba a cikin hukumonin da batun ya shafa a yayin wani taron karawa juna sani da aka bude kwanan nan a birnin Lome na kasar Togo.

Bankin BOAD ya yi wannan kira a cikin wani bayani da ya gabatar a yayin taron da ya shafi bincike kan wani sakamakon tattalin arziki da jama'a da ya rataya kan wasu ayyukan noma da ruwa guda bakwai da bankin ya zuba kudin gudanar da su a cikin kasashe hudu da suka hada da Burkina Faso, Mali, Nijar da kuma Senegal.

Binciken na da manufar gano wani salo na musamman da zai raya wadannan ayyukan noma da ruwa a cikin shiyyar kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika wato UEMOA, dake kunshe da hekta miliyan 2,6 na filayen noma da a cikinsu kashi 21 cikin 100 ne kawai ake amfana da su wajen ayyukan noma, in ji bankin BOAD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China