in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zama abun koyi ga kasashe masu tasowa a fannin noma, in ji shugaban IFAD
2014-02-20 14:11:10 cri

Shugaban asusun bunkasa ayyukan noma na kasa da kasa IFAD, Kanayo Nwanze, ya ce, kasar Sin ta zama abun koyi ga kasashe masu tasowa a fannin bunkasa harkokin noma.

Nwanze wanda ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, a taron hukumar gudanarwar asusun na shekara shekara karo na 37, ya ce, baiwa tsarin zuba jari mai dogon zango muhimmanci, da wanzar da manufofi bisa tsari, tare da aiwatar da managartan sauye-sauye a tsarin noma daga matakin farko da kasar Sin ke yi, ya sanya ta zama abun kwatance ga sauran kasashe masu tasowa.

Shugaban asusun na IFAD ya kara da cewa, tsare-tsaren bunkasa noma daga tushe, da tallafawa kananan manoma, ya baiwa Sin damar samun ci gaba cikin gaggawa, ta yadda a yanzu haka ta kai ga matsayi na biyu a bunkasar tattalin arzikin duniya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China