Cibiyar binciken ta bayyana hakan ne, cikin rahoton ta game da yanayin aikin noma na kasar Sin a nan gaba, tsakanin shekarun 2014 zuwa 2023, wanda kuma ta gabatar a ranar 20 ga wata. Rahoton ya nuna cewa daukar wannan mataki ne, zai sa Sin ta iya cimma burinta a fannin samar da isashen abinci a gida.
Kaza lika rahoton ya shaida cewa, cikin shekaru 10 masu zuwa, tsarin kasuwanni na zamani, da matakan da gwamnati ta dauka don raya aikin noma, gami da cigaban kimiya da fasaha, za su rika samar da yanayi mai kyau na raya aikin noma a kasar.
Yayin kuma da ake samun karuwar kayayyakin amfanin gona a kasar, madara da sauran abinci masu alaka da ita za su zama mafiya saurin karuwa bisa adadin da ya kai kaso 3.5 bisa dari a ko wace shekara. (Bello Wang)