Gwamnatin Afrika ta Kudu ta sanar a ranar Talata cewa, ta kaddamar da wani shirin kasa domin bunkasa noma da tsaron abinci, bisa kokarinta na kawar da talauci da yunwa. Kuma ana tafiyar da shirin a karkashin jagorancin ma'aikatar cigaban al'umma, a cewar ministar noma madam Tina Joemat-Petterson a yayin wani taron manema labarai a birnin Johannesburg. A cikin tsarin wannan shiri, manufar bunkasa noma ita ce neman filayen noma masu kyau da ba'a yawan amfani da su a cikin kasar da kuma za'a iyar amfani da su wajen samar da abinci, in ji ministar tare da jaddada muhimmancin noma wajen rage talauci, kuma a cikin wannan wata ne gwamnatin Afrika ta Kudu za ta ba da sanarwar bude lokacin yin shuke-shuke na shekarar 2013 zuwa ta 2014, ta yadda za'a iyar baiwa jama'a kwarin gwiwa na shuka kayayyakin lambu da hatsi a cikin gonakinsu. A karshen wannan shiri, wasu kayayyakin da aka noma za'a rarrabawa talakawa, yayin da sauran za'a shigar da su kasuwanni.
A lokacin da take bayyana niyyarta wajen yaki da talauci a Afrika ta Kudu, madam Joemat-Petterson ta nuna cewa, gwamnatin kasar ta yi imanin cewa, wannan shiri zai dauki babban matsayi wajen kawar da talauci da bunkasa tattalin arzikin yankunan kasar baki diya. (Maman Ada)