in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika za ta fuskanci karancin abinci nan da shekaru 20 idan babu zuba jari a fannin noma
2014-05-13 10:56:38 cri

Nahiyar Afrika za ta fuskanci matsalar karancin abinci nan da shekaru 15 zuwa 20 masu zuwa, sai in kuma za'a dauki kwararrun matakai domin bunkasa aikin noman nahiyar, in ji ministan noman tarayyar Najeriya Akinwumi Adesina a cikin wata hirarsa tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Wata muhimmiyar niyya ta zama wajibi domin zuba kudi ga aikin noma da abinci, da kuma kara shigar da matasan nahiyar cikin aikin noma, idan ba da haka ba, to za'a fuskanci matsaloli masu tsanani.

Mista Adesina ya yi wannan rigakafi jim kadan bayan tattaunawa kan batun zuba jari a fannin noma a matsayin hanyar samun cigaba, a albarkacin dandalin tattalin arzikin duniya kan Afrika na baya bayan nan da aka shirya a Abujan, inda ya yi kira da a canja salon kallon da matasa suke wa noma domin wani bangaren tattalin arziki ne dake iyar samar da guraben aikin yi da arziki.

Ba na tsammanin Afrika na fatan rika shigo da abinci daga kasashen waje. Ya kamata Afrika ta farfado da filayen noman da ta yi watsi da su. Amma matsalar da muka fuskanta ita ce mun dauki noma a matsayin wani aikin cigaba, a maimakon wani bangaren tattalin arziki, in ji wannan jami'i.

Najeriya ta canja ra'ayi kan noma, kuma ta dauke shi a matsayin wani bangaren tattalin arziki, abin dake ba da damar yin amfani da wannan arziki daga dukkan fannoni.

Domin ciyar da kan mu, ya zama dole Afrika ta kara yawaita amfani da fasahohin zamani, irin shuka masu inganci, da taki maras gurbata muhalli, gaggauta zuba jari domin samar da ruwa da gine-gine a wannan fanni a yankunan karkara da kuma gaggauta samar wa manoma kudin tafiyar da harkokinsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China