Gwamnatin tarayyar Najeriya na aiki kan wasu shirye-shiryen rage shigowa da alkama cikin kasar da kashi 20 cikin 100, in ji ministan noman kasar mista Akinwumi Adesina.
Ministan ya bayyana shirin dake nuna amfani da garin rogo wajen sarrafa burodi kuma yin haka zai taimaka wajen kebe fiye da dalar Amurka miliyan 796 a kowace shekara, tare da wasu sauran ayyuka masu alfanu kamar bunkasa noman rogo da bunkasa masana'antun sassafa rogo tare da kyautata aikin yi.
Bisa karfin sarrafa tan miliyan 40 a kowace shekara, Najeriya ta kasance kasa ta farko wajen noman rogo a duniya a yayin da kasar Thailande ta zama babbar kasa a duniya wajen fitar da busasshen rogo.
'Mun fahimci dalilin Thailande dake kasa ta uku a fannin noman rogo ta mamaye kashi fiye da 80 cikin 100 na wannan kasuwa a duniya. Ke nan ya zama wajibi gare mu da daukar nauyinmu a matsayin kasa ta farko a wannan sana'a.' in ji mista Adesina.
Gwamnatin Najeriya ta amince da wani asusun dalar Amurka miliyan 63 tare da wasu tsare-tsaren horar da masu sana'ar yin burodi domin yin amfani da garin rogo, ta yadda za'a bunkasa noman rogo a cikin kasar, in ji wannana jami'i. (Maman Ada)