in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da taimakon bunkasa aikin noma a Cape Verde
2014-04-08 10:04:46 cri

Jakadan kasar Sin da ke kasar Cape Verde ya baiwa ma'aikatar bunkasa aikin noma da cigaban karkara ta kasar wasu kayayyakin samar da ruwa a yankunan karkara a ranar Litinin da aka kiyasta darajarsu zuwa fiye da dalar Amurka miliyan 1,58 in ji wata majiya mai tushe a birnin Praia.

A cewar jakadan kasar Sin, Su Jian, wadannan kayyayaki kamar na bincike, suna iya kara samar da ruwa domin aikin noma, musammun ma a yankunan da ake noman rani. Kasar Sin, a cewar mista Su Jian, tana da wasu shirye-shiryen ayyukan ciyar da dangantaka tsakaninta da Cape Verde, kuma nan da 'yan shekaru masu zuwa, za'a baiwa noma, kiwon lafiya da ilimi fiffiko. A shekarar 2014, bangarorin biyu suna fatan kara gudanar da ayyuka tare, musamman wajen gina cibiyar sarrafa kayayyakin gona kusa da madatsar ruwa ta Poilao, aikin kyautata da kara darajar kayayyakin gona da ake nomawa a wannan yanki.

A cewar ministar noman Cape Verde, madam Eva Ortet, wadannan kayayyaki da kasar Sin ta samar za su taimaka wajen binciken samar da ruwa, haka rijiyoyi, shayar filayen noma ta hanyar digon ruwa dake da wani muhimmin tsari a wannan kasa. Haka kuma ta nuna cewa, kasar Cape Verde tana bukatar kayayyaki da taimakon fasaha wajen kwashe kasa da kuma sanya ido kan madatsun ruwa, tare da kwararrun kasar Sin a fannoni daban daban domin taimakawa bangaren noma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China