in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin ayyukan noma na kauyukan Sin na bunkasa cikin yanayi mai karko
2013-07-22 11:00:08 cri
Cikin farkon rabin shekarar bana, an samar da karin hatsi a kasar Sin, manoma sun sami karin kudaden shiga, ayyukan da ke shafar kiwon dabbobi sun samu bunkasuwa bayan magance cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9, kana an samu isassun kayayyakin noma a kasuwanni. Watau lamarin ya nuna mana cewa, tattalin arzikin ayyukan noma na kauyukan kasar Sin na ci gaba da bunkasa, wanda ya taimaka ga samun karuwar tattalin arziki mai dorewa, da hana hauhawar farashin kayayyaki da kuma kiyaye kasuwannin kayayyakin noma a kasar Sin.

Ran 21 ga wata, yayin taron direktocin hukumomin ayyukan noma na fadin kasar da aka kira a birnin Taiyuan, ministan kula da harkokin noma na kasar Sin, Han Changfu ya bayyana cewa, cikin shekarar bana, gwamnatin tsakiya ta fidda wasu sabbin manufofi masu inganci don karfafa ayyukan noma, ba da taimako ga manoma da kuma kara musu kudaden shiga, ya kamata hukumomin kula da ayyukan noma na wuraren daban-daban na kasar su yi amfani da manufofin da aka fitar, domin sabunta tsarin alawas na sayan na'urorin ayyukan noma ta yadda za a iya ciyar da tattalin arzikin ayyukan noma na kauyukan kasar Sin gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China