Kasar Tanzaniya za ta karbi bakuncin wani taron kasa da kasa kan noma a Afrika a yayin da ake fuskantar sauyin yanayi tare da halartar kwararru daga kasashen Afrika 20, in ji wani jami'in kasar Tanzaniya a ranar Lahadi.
Mweusi Karake, mai kula da shirin rage kaifin illolin sauyin yanayi a shiyyar kudu maso gabashin Afirka, ya nuna cewa, za'a bude wannan taro a ranar Talata a birnin Arusha, ya jaddada cewa, kwararru za su yi musanyar fasahohin da suka shafi samun cigaba da aiwatar da manufofin kasashe a wannan fanni, dabaru da kuma tsare-tsaren ayyuka domin fuskantar sauyin yanayi.
Mahalartan taron za su kuma duba hanyoyin karfafa hadin gwiwa tsakanin matakan da ake dauka kan sauyin yanayi da noma, sannan za su kimanta shirye-shiryen kasashen Afrika wajen samun kudade da za su zuba a wannan fanni, bullo da nagartattun ayyuka, ta yadda za a iya raya aikin gona na zamani a duk fadin duniya. (Maman Ada)