Yau Jumma'a 14 ga wata da safe ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa birnin Brisbane na kasar Australia don halartar taron shugabannin kungiyar G20 karo na tara bisa gayyatar da firaministan kasar Australia Tony Abbott ya yi masa. Haka kuma, Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasashen Australia, New Zealand, da kuma Fiji bisa gayyatar da shugabannin kasashen uku suka yi masa, bugu da kari, zai gana da shugabannin tsibiran kasashen tekun Pacific da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin a yayin ziyarar da ya kai kasar Fiji.
Daga cikin wadanda suka rufawa shugaba Xi baya yayin ziyarar, sun hada da uwargidansa Peng Liyuan, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, shugaban ofishin nazarin manufofin kwamitin tsakiya na JKS Wang Huning, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Wang Yang da dai sauransu. (Maryam)