in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun gana da juna a karo na 2 cikin watanni 3
2013-09-06 20:17:00 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun gana da juna a yau Jumma'a 6 ga wata a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, inda suka tattauana kan batutuwan da suka fi jawo hankalin kasashen biyu.

A lokacin ganawar shugaba Xi ya ce, wannan lokaci ya tuna masa da ganawarsu watanni uku da suka gabata, inda suka yi musayar ra'ayi kan hanyoyin da kasashensu za su bi domin inganta hadin gwiwa tare da juna. Ya ce, kasarsa da ta Amurka suna kokarin aiki tare don ganin sun aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a lokacin ganawarsu ta baya. Xi yana mai nuni da cewa, tuni ma har an fara samun sakamako mai gamsarwa a taron koli karo na biyar da aka yi domin tattaunawa a kan manyan tsare-tsare da harkokin tattalin arziki a watan Yulin da ya gabata.

Sin da Amurka, in ji shi, suna ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba masu ma'ana, abin da ya sa ya lura da cewa, kasashen biyu sun samu ci gaba ta fannin huldar tsakanin sojojinsu, kuma suna ci gaba da cudanya da juna da hadin gwiwa a kan harkokin da suka shafi duniya da yankunan shiyoyi daban daban.

A nasa bangaren shugaba Obama ya lura da cewa, kasashen biyu sun samu ci gaba sosai a bangaren hadin gwiwa ta ayyukan da suka shafi canjin yanayi da kuma karfafa cudanya ta bangaren soja, inda ya tabbatar da cewa, kasashen biyu sun amince su kafa sabon tsari mai karfi bisa ga hadin gwiwa ta zahiri domin gyara da daidaita bambance-bambancen dake tsakaninsu.

Wannan ganawa dai tsakanin shugaba Xi Jinping na kasar Sin da Barack Obama na Amurka ita ce ta biyu a cikin watanni 3.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China