in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaban kasar Sin a taron kolin G20
2013-09-06 09:20:14 cri

A ranar 5 ga wata, an yi taron koli karo na 8 na kasashe mambobin kungiyar G20 a birnin Saint Peterburg da ke kasar Rasha. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wannan taro, inda ya bayar da jawabinsa.

A cikin jawabinsa, Mr. Xi ya bayyana cewa, yanzu, tattalin arzikin duniya na samun farfadowa, kuma halin da ake ciki ya fara inganta yadda ya dace. A sa'i daya kuma, ya kamata a yi la'akari da cewa, irin mummunan tasirin da rikicin kudi na duniya ya haifar na ci gaba da kasancewa, shi kuma ya nuna cewa, akwai sauran rina a kaba wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Don haka dole ne kasashen duniya su yi kokarin kirkiro da sabbin manufofi, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da samun moriyar juna tare.

Shugaban Xi ya jaddada cewa, domin cimma burin raya tattalin arzikin duniya, kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar G20 su raya dangantakar abokantaka da ke tsakaninsu cikin aminci, da daukar alhakin da ke wuyansu yadda ya kamata.

A karshe dai, Mr. Xi ya nanata cewa, domin cimma burin raya tattalin arzikin kasar Sin, kasarsa za ta nace kan karfafa aikin yin kwaskwarima. Haka kuma, yanzu, muna yin nazari game da aikin yin kwaskwarima daga manyan fannoni, don aiwatar da hakan a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da zamantakewar al'umma, da kuma kiyaye muhallin halittu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China