Shehun malami a kwalejin koyon hada-hadar kudi na Frankfurt da ke kasar Jamus Horst Löchel ya bayyana cewa, a matsayin wata babbar kasa wadda ta samu bunkasuwa cikin hanzari, kuma wakilin kasashe masu saurin bunkasuwa, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a yayin taron koli na G20. Tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa lami lafiya, kuma zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen yaki da rikicin kudi na duniya, da sa kaimi ga farfado da tattalin arziki.
Shehun malami a sashen tattalin arziki na jami'ar Mexico Alejandro Martínez ya bayyana cewa, a matsayin gamayyar tattalin arziki mafi girma ta biyu a duniya, kasar Sin ta dauki matakan hadin gwiwa yadda ya kamata a karkashin inuwar kungiyar kasashen G20. Yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashe masu wadata da kasashe masu tasowa, don sa kaimi ga samun daidaito a tsakaninsu.(Bako)