Shugaba Xi ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a gaban mahalarta taron koli na kungiyar G20 a ranar Jumma'a 6 ga wata, yana mai cewa, hada-hadar cinikayyar kasa da kasa na fuskantar tarin kalubale, ciki hadda kiki-kakar da aka fuskanta yayin taron Doha, da batun sanya shinge ga cinikayyar kasa da kasa, matsalolin da suka yi amanar cewa, an haifar da koma-bayan tattalin arziki ga kasashen duniya, tare kuma da kawo tsaiko ga burin farfadowar tattalin arzikinsu.
Dangane da wannan batu, shugaban na kasar Sin na ganin ya zama wajibi ga shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar ta G20 da ke jagorantar hada-hadar kasuwanci da ta kai ga kaso 80 bisa dari a fadin duniya, su daura damarar shirya wani managarcin shiri da zai ba da damar fadada harkokin kasuwanci da cinikayyar kasa da kasa.
Shugaba Xi ya kuma gabatar da wasu shawarwari guda uku ga taron na G20, wadanda a cewarsa, za su yi matukar taimakawa wajen inganta halin da ake ciki. Shawarwarin kuwa sun hada kira ga mambobin G20 da su goyi bayan daukar matakan baiwa kasuwa ikon cin gashin kai, da kau da shingayen dake dalike harkokin cinikayya cikin 'yanci. Sai kuma batun karfafa yarjeniyoyin cinikayyar kasa da kasa, da sake ci gaba da tattaunawa kan kudurorin taron Doha da aka jingine. Har ila yau shugaban kasar ta Sin ya ba da shawarar daukar matakan bunkasa dunkulewar kasuwannin duniya, ta yadda hakan zai iya samar da moriya ga kowa.
Ban da wannan ma, shugaba Xi na ganin akwai bukatar kasashe mambobin G20 su shirya manufofin agazawa kasashe masu tasowa, da fasahohin habaka harkokin cinikayyarsu. Bisa hakan ne ma ya ce, kasarsa ta samar da tanajin yafe harajin kaso 95 bisa dari kan kayayyakin da kasashe masu raunin tattalin arziki ke shigarwa kasar ta Sin, tare da fatan kara wannan adadi zuwa kaso 97 bisa dari nan da shekarar 2015.
Daga nan sai ya yi alkawrin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da manufofin da za su kawo daidaito ga ci-gaba harkokin cinikayyar kasa da kasa, su kuma ba da damar ci gaba da bude kofarta ga kasashen ketare, duka dai da burin ganin cinikayya tsakanin kasar da kasashe mambobin G20, da ma ragowar kasashen duniya ta haifar da moriya ga ko wane sashe, tare da ci-gaba mai dorewa ga duniya baki daya.(Saminu)