Dangane da wannan taro, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi karin haske, inda ya ce, yayin taron na wannan karo, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, wanda a cikinsa ya gabatar da jerin sabbin ra'ayoyi, da yin kira ga kasashe membobin kungiyar G20 da su kafa dangantakar abokantaka tsakaninsu, da yin hadin gwiwa, tare da yin takara tsakaninsu, a kokarin samun moriyar juna.
Ra'ayoyin shugaba Xi sun samu karbuwa kwarai ga sauran kasashe mahalarta taron, kuma an shigar da wasu daga cikinsu cikin sanarwar shugabannin taron koli na kungiyar ta G20 na wannan karo. Shugaba Xi ya bayyana ikon kasar Sin na fada-a-ji, tare da daga matsayin kasar a fannin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.
Ban da haka, Wang ya kara da cewa, a gun taron, shugaba Xi ya gabatar da makomar kasar Sin a fannin raya tattalin arziki, inda ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfi da kuma kwarewa wajen tabbatar da bunkasar tattalin arziki mai dorewa cikin lumana, tare da kara ba da gudummawa ga duniya a wannan fanni. Game da wannan batu, ana ganin cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a gida yadda ya kamata. Bayan kyautatuwar tattalin arzikinta dake karuwa, kasar Sin za ta ci gaba da samun makoma mai kyau, wanda hakan ka iya zama babban zarafi ga duniya baki daya. (Fatima)